✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nada Alhaji Ahmed Mohammed Usman sabon Sarkin Deba

Gwamnatin Jihar Gombe ta nada Alhaji Ahmed Mohammed Usman a matsayin sabon Sarin Deba. Sabon Sarkin ya gaji marigayi Sarkin Deba Laftana Kanar Abubakar Waziri…

Gwamnatin Jihar Gombe ta nada Alhaji Ahmed Mohammed Usman a matsayin sabon Sarin Deba. Sabon Sarkin ya gaji marigayi Sarkin Deba Laftana Kanar Abubakar Waziri Mahdi, Sarki na 36 wanda ya rasu a ranar Alhamis 23 ga Maris din bana. Kwamishinan Kasanan Hukumomi da Harkkokin Masarautu na Jihar Gombe, Alhaji Ahmed Abubakar Walama ne ya mika wa sabon Sarkin takardar nada shi a sarautar  a ranar Talatar da ta gabata, inda ya zama  Sarkin Deba na 37 kuma Sarkin yanka na 2 a masarautar.

Kafin nada Alhaji Ahmed Mohammed Usman, shi ne Daraktan Sashin Kula da bin Ka’idoji a Gwamnatin Jihar Gombe.

An haifin sabon Sarkin ne a ranar 23 ga Oktoban a 1963 a garin Deba kuma ya yi karatu a F iramaren Central ta Deba a 1970 zuwa 1976 daga nan ya tafi Sakandaren Gwamnati ta Bauchi a 1976 zuwa 1981 bayan ya gama sai ya wuce zuwa Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, a tsakanin  ta 1982 zuwa 1986 inda ya samu Digiri a ilimin safiyo.

Alhaji Ahmed Mohammed Usman, ya rike mukamai da dama ciki har da shugaban sashin kula da sanin darajar kadarori da ke Abuja sannan ya zama mataimakin darakta a Hukumar Bunkasa Yankunan kan  Iyaka (Boarder Communities Debelopment Agency) a shekara ta 2010 zuwa 2011, daga nan sai ya zama babban mai taimaka wa Gwaman Jihar Gombe a bangaren kula da bin ka’idoji waen bayar da kwangilolin gwamanti wato Due Process.

Ya zaman Darakta a wannan sashi a shekara ta 2015 zuwa yanzu da aka nada shi ya sabon Sarkin Deba mai daraja ta 1a ranar Talata 8 ga watan Agusta.

Shi dai marigayi Sarki Laftana Kanar Abubakar Waziri Mahdi, ya karbi sarauta ce a 1984 inda ya gaji kakansa. Marigayin tsohon soja ne da ya kai mukamin Laftana Kanar kafin ya zama Sarki.