✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nada alkali mai sa hijabi ta farko a Birtaniya

An nada Musulma mai sanya hijabi ta farko a matsayin alkalin kotu a kasar Birtaniya. Raffia Arshad ita ce Musulma da ke sanya hijabi ta…

An nada Musulma mai sanya hijabi ta farko a matsayin alkalin kotu a kasar Birtaniya.

Raffia Arshad ita ce Musulma da ke sanya hijabi ta farko da ta taba zama alkali a Birtaniya.

Sabuwar alkalin mai shekara 40 ta zama alkali a yankin Midland bayan shafe shekara 17 tana aikin sharia.

Jaridar Indepent ta ambato Raffia na shaida wa Metro cewa a baya ta dauka matsayin iyayenta da kasancewarta daga al’umma marasa rinjaye za su zama mata kalubale a fannin sharia.

“Wannan nasarar ba tawa ba ce ni kadai. Nasara ce ga dukkan mata musamman Musulmai, har ma da wadanda ba Musulmai ba,” inji ta.

Raffia ta yi alkawarin amfani da sabon matsayinta wurin yin adalci da bayar da murya ga kowane bangare.

Ta bayyana yadda takwarorinta masu sanya hijabi suka mara mata baya a matsayin abin da ya fi faranta mata rai game sabon matsayin nata.

“Mutane da dama, maza da mata sun yi ta aiko mini da sakon taya murna.

“Wadanda suka fi daukar hankalina su ne mata masu hijabi da a baya suke ganin ko lauya ba za su iya zama ba, ballantana alkali,” a cewarta.
A shekarar 2004 Alkali Raffia ta fara aiki da ofishin shari’a na St Mary’s Family Law Chambers.

A shekaru 17 na aikinta a fannin ta samu gogewa a Shariar Musulunci, hakkin yara, cin zarafi da kuma auren dole.

Sai dai ta ce duk da haka ta fuskanci nau’uka tsangwama. Ta bayyana yadda a wani lokaci wani akawun kotu ya yi mata kallon mai aikin tafinta a cikin zauren kotu.