Da Dumi Dumi

An nada Jose Mourinho a matsayin kocin Tottenham

Jose Morinho sabon Kocin Tottenham

An nada Jose Mourinho a matsayin sabon kocin Tottenham inda ya maye gurbin Mauricio Pochettino wanda aka kora daga kan mukamin a ranar Talata.

Tsohon kocin Chelsea da Manchester United, Mourinho ya sanya hannu kan kwantaragi zuwa karshen kakar wasa ta 2022-23.

“Ingancin ayari da makarantar koyar da ’yan wasan kungiyar sun burge ni,” inji dan kasar ta Portugal mai shekara 56. Ya ci gaba da cewa “Yin aiki da wadannan ’yan wasa shi ne abin da ya fi jan hankalina.”

Kamar yadda sashin Hausa na BBC Landan ya ruwaito, mamallakin Kungiyar Spurs Daniel Leby ya ce: “Samun Jose na nufin samun daya daga cikin manajojin da suka yi nasara a kwallo.”

Tottenham ta kai matakin wasan karshe a Gasar Zakarun Turai a bara a karkashin Pochettino, amma Liberpool ta yi nasara a kanta da ci 2-0 a Madrid.

ADVERTISEMENT

Kocin dan kasar Ajantina, wanda aka nada shi a watan Mayun 2014, bai ci kofi ko daya ba a lokacin da ya jagoranci kungiyar, wadda rabonta da yin wata nasara tun lokacin da ta zo ta biyu a gasar League Cup a shekarar 2008.

Leby ya ce Mourinho “Yana da kwarewa, kuma zai iya zaburar da kungiyar kuma yana da lissafin cin wasanni.”

“Ya samu martaba a duk wata kungiya da ya jagoranta. Mun yi amanna zai kara wa ’yan wasan kwarin gwiwa,” inji shi.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya