Da Dumi Dumi

An nada Kwamared Garba Ubale Kainuwan Akko

Komred Garba Ubale Kainuwan Akko
Komred Garba Ubale Kainuwan Akko

A makon jiya ne Mai martaba Sarkin Akko da ke Jihar Gombe, Alhaji Umar Muhammad Atiku ya nada tsohon Shugaban Kungiyar Matasan Najeriya (NYCN) reshen jihar kuma Mataimakin Shugaban shiyar Arewa maso Gabas, kuma mamba a Hukumar Jin Dadi da Walwalar matasa ta Jihar Gombe a matsayin Kainuwan Akko na farko. Sabon Kainuwan Akkon, shi ne Shugaban Kungiyar Zabi Sonka da Taimakon Juna ta Kasa reshen Jihar Gombe, kuma an nada shi ne a kan sarautar saboda gudunmawar da yake ba Masarautar Akko kamar yadda Mai martaba Sarkin Akko Alhaji Umar Muhammad Atiku, ya bayyana, don kara jawo shi kusa da fada domin ya ci gaba da taimaka wa masarautar.

Da yake nada Kainuwan na Akko Sarkin ya yi kira ga masu rike da sarautun gargajiya a masarautar su ci gaba da bai wa masarautar hadin kai da goyon baya da kawo mata abubuwan ci gaba kamar yadda Kwamared Ubale yake yi kuma ya bukaci Kainuwan ya kara kokari kan wanda yake yi.

Alhaji Umar Atiku, ya bayyana Kwamared Garba Ubale, a matsayin mai da`a da biyayya ga gwamnati da fada, sai ya shawarce shi, kan ya ci gaba inda ya nemi jama’a su taya shi da addu’a.

Da yake tsokaci, Majidadin Akko Alhaji Ahmed Musa Kumo, ya shawarci Kainuwan Akkon da kada ya gaza wajen ci gaba da ayyukan madalla da yake kawo wa masarautar da yadda yake mutunta ta da sauran ’yan Majalisar Sarki.

A jawabin godiya tsohon Babban Sakatare a Jihar Alhaji Umaru Gurama gode wa Sarkin ya yi da ’yan majalisarsa bisa yadda suka ga kwazon Garba Ubale aka nada shi daya daga cikin ’yan Majalisar Sarkin.

ADVERTISEMENT

Kainuwan na Akko Kwamared Garba Ubale, ya ce ba ya da kalmar da zai iya gode wa Sarkin da ’yan majalisarsa sai dai ya yi addu’ar Allah Ya kara wa Sarki lafiya Ya kuma kara kawo wa masarautar Akko da Jihar Gombe ci gaba.

Nadin Kainuwan ya jawo jama’a a ciki da wajen Jihar Gombe musamman ’yan uwa da abokin arziki daga kungiyoyin PCRC da  zabi sonka na kasa da NYCN da sauransu.

Share