✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nada Kyaftin Yadudu Daraktan Hukumar FAAN

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya amince da nada Kyaftin Rabiu Hamisu Yadudu  a matsayin sabon Manajan Daraktan hukumar kula da tashoshin jiragen sama ta Najeriya…

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya amince da nada Kyaftin Rabiu Hamisu Yadudu  a matsayin sabon Manajan Daraktan hukumar kula da tashoshin jiragen sama ta Najeriya FAAN.

Kyaftin Yadudu zai maye gurbin Injiniya Saleh Dunoma wanda aka dakatar, kamar yadda mataimakin Daraktan hulda jama’a da sadarwa na ma’aikatar sufuri (Sashen jiragen sama) James Odaudu, ya sanar.

Sanarwar ta kara da cewa, mukamin sabon Daraktan zai fara aiki ne nan take.