✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nada Sarkin Hausawa a fadar Ooni na Ife

Ranar Asabar din makon jiya ta zamo tamkar ranar hawan idi ga al’ummar Hausawan garin Ile-Ife inda maza da matansu da yara cikin sababbin tufafi…

Ranar Asabar din makon jiya ta zamo tamkar ranar hawan idi ga al’ummar Hausawan garin Ile-Ife inda maza da matansu da yara cikin sababbin tufafi suka yi dafifi a fadar Ooni na Ife Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, Ojaja II,  don nada musu sabon Sarkin Hausawa Ile-ife Alhaji Lawal Isiyaka Yaro a fadarsa. Fadar Ife ce  mafi girma da daraja a daukacin jihohin Yarbawa, kuma Oonin ne Sarki mafi girma da daukaka a jihohin Yarbawa.                                                                                                                                              Al’ummar Hausawan garin Ile-Ife sun samu kyakkyawar tarba a fadarsa inda ya gutsura musu kadan daga cikin tarihin garin na Ife da masarautarsa. Ya ce ma’anar sunan garin ta samo asali ne daga kalmar soyayya, domin a harshen Yarbanci kalmar ‘Ile’ na nufin gida,  ‘Ife’ kuma na nufin so, “Idan ka hada kalmaomin biyu za su ba da sunan garinmu wato Ile-Ife ma’anar “Gidan Soyayya,” don haka wannan gari na son baki ne da zaman lafiya,” inji Ooni na Ife.

Ooni na Ife ya nuna farin ciki kan yadda al’ummar Hausawa suka hada kai suka zabi daya daga cikinsu domin ya zamo jagoransu bayan rasuwar Sarkinsu Alhaji Mamuda Lawal Madagali kimanin wata uku da suka shude inda ya yi kira ga sabon Sarkin Hausawa Alhaji Lawal Isiyaka Yaro ya yi wa al’ummarsa jagoranci nagari, kuma ya tafi da kowa a mulkinsa ba tare da nuna bangaranci ba.

A zantawarsa da Aminiya sabon Sarkin Hausawan Alhaji Lawal Isiyaka Yaro ya ce abu na farko da zai maida hankali a kai shi ne zaman lafiyar al’ummar  Hausawan da yake yi wa jagoranci da abokan zamansu Yarbawa da daukacin mutanen yankin. Kuma abu na biyu shi ne samar wa matasa ayyukan yi. “Akwai matasanmu da dama da ba su da abin yi, muna duba hanyoyin da suka kamata mu bi wajen sama musu ayyukan dogaro da kai. Fatarmu Allah Ya shige mana gaba mu samu mu rage matasa masu zaman dirshan. Wannan ne ya sa muka yi yunkurin neman kasuwa kuma mun samu wata karama mun bude ta a ranar 15 ga watan jiya  kuma yanzu haka kasuwar tana ci ana samun ci gaba, matasanmu na zuwa, kuma muna ci gaba da neman babban wuri mun mika kokon bararmu ga Mai martaba Ooni na Ife. Muna so ya ba mu kasa yalwataciyya mu yi kasuwar duniya irin wadanda ake da su a Legas kamar Kasuwar Shanu ta Abbatuwa da Kasuwar Kayan Gwari ta Mil 12 a Legas. Da yarda Allah in aka kai ga haka za a samu saukin zaman kashe wando a tsakanin matasanmu” inji shi.

Ya ce shi da Allah Ya ba sarautar da wadanda suka nema tare da shi ba su samu ba babu wanda ya yi asara. Nasararsa nasara ce ga dukkansu don haka su zo a hadu a yi wa jama’a aiki domin ci gaban al’ummar garin Ile-Ife.

Bikin nadin Sarkin Hausawan ya samu halartar sarakunan Hausawa da na Fulani daga jihohin Kudu maso Yamma da kuma jihohin Edo da Delta, ciki har da Sarkin Hausawa Ire Alhaji Abdullahi Bagobiri da Shugaban ’Yan Arewa Mazauna Jihar Ekiti Alhaji Adamu Imam da Alhaji Shehu Abdullahi sarkin Hausawan Shaha Akure da wakilin Sarkin Sasa Sardaunan Yamma Alhaji Haruna Mai Yasin da na Sarkin Hausawan Ibadan da sauransu, wadanda suka yi wa Alhaji Lawal Isiyaka Yaro fatar alheri tare da rokon Allah Ya yi masa jagora.