✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nada sarkin kabilar Igbo a Masarautar Jama’a

Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad II ya nada Mista Richard Ogbonna a matsayin Sarkin Kabilar Igbo (Eze Igbo) na II da kuma…

Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad II ya nada Mista Richard Ogbonna a matsayin Sarkin Kabilar Igbo (Eze Igbo) na II da kuma Mista Decline Benco a matsayin Sarkin Kabilu da ke Masarautar Jama’a a Karamar Hukumar Jama’a da ke Jihar Kaduna.

Nadin, wanda aka gudanar a fadar sarkin jim kadan bayan idar da sallar jumma’a, ya samu halartar mutane da dama.

Da yake jawabi jim kadan bayan kammala nadin, Mai Martaba Sarkin Jama’a ya yi kira ga ‘yan kabilar ta Igbo da ke da tsohon tarihin zaman lumana da masarautar, da su ci gaba da baiwa masarautar hadin kai da kuma zaman lumana domin, a cewarsa, harkokin kasuwanci da na siyasa suna wakana ne kawai idan akwai zaman lafiya, inda yayi kira ga jama’a musamman lokacin karatowar zabukan 2019 da kowa ya fita ya kada kuri’arsa ba tare da hantarar juna ko neman tada fitina ba.

Bayan kammala nadin, an dora su a kan dawakai inda aka kewaya da su cikin gari tare da kade-kade da bushe-bushe kafin aka raka kowa zuwa gidansa.

A lokacin da yake jawabi a bukin da ya shirya a kofar gidansa da ke Unguwar Hayin Gada, sabon Eze na kabilar Igbo, Mista Richard Ogbonna ya fara mika godiyarsa ne ga Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad II da ya karrama kabilar Igbo da ba su sarkinsu wanda hakan ya gaji mahaifinsa ne marigayi Sarki Alhaji Isa Muhammad Sani da ya fara nada musu sarki a masarautarsa wanda shi kuma yanzu ya gaji tsohon sarkin na Igbo, Eze Chima Okoli, da tsufa ta sa ya ya tattara ya koma kasarsu.

Ya ce wannan karamci da ake nuna wa kabilar ta Igbo abin yabawa ne.

Sabon Eze na Igbo, wanda har ila yau shi ne Sakataren kungiyar ’yan kasuwa na garin Kafanchan, ya yi kira ga wadanda suka nemi sarautar ba su samu ba da su rungumi kaddara su zo su ba shi hadin kai kamar yadda ya yi alkawarin tafiyar da kowa cikin adalici.