✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nada Sarkin Makafin Masarautar Jama’a

A ranar Juma’ar da ta gabata ce aka nada Malam Muhammad Bello Umar  sabon Sarkin Makafin Masarautar Jama’a a fadar Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji…

A ranar Juma’ar da ta gabata ce aka nada Malam Muhammad Bello Umar  sabon Sarkin Makafin Masarautar Jama’a a fadar Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad II da ke garin Kafanchan, hedkwatar Karamar Hukumar Jama’a da ke Jihar Kaduna.

Da yake tattaunawa da Aminiya bayan kammala nadinsa, sabon Sarkin Makafin, ya mika godiyarsa ga Allah Ya kuma jinjina wa Mai martaba Sarkin Jama’a da kuma ’yan uwansa makafi da suka ba shi goyon baya har zuwa kammaluwar bikin lafiya.

Sarkin Makafin, ya kuma yi kira ga shugabanni tun daga na kananan hukumomi  zuwa Gwamna da Shugaban Kasa da kungiyoyi kan su rika daukar nauyin karatun ’ya’yan nakasassu maimakon barinsu a baya da ake yi a dukkan nau’in tallafi da gwamnatoci ke bayarwa.

“Maimakon a rika zargin muna kwashe ’ya’yanmu muna zuwa yawon bara da su, kamata a ce gwamnati ta samar wa ’ya’yanmu da wata gidauniya da za ta rika tallafa wa ’ya’yanmu wajen yin karatu har zuwa gaba da sakandare. Ka ga ni ina da yara shida kuma cikinsu akwai wanda ya kammala sakandare kuma burinsa shi ne ya ci gaba da karatu a kwaleji ko jami’a tunda ya fito da sakamako mai kyau amma babu hali kuma babu wani tallafi,” inji shi

Sarkin Makafin ya ce babu wani tallafi kowane iri ne da suke jin labari gwamnati na badawa da ya taba zuwa hannunsu musamman wannan gwamnati da ke kokarin tallafa wa mata da matasa da kuma nakasassu, inda yayi kira su rika waiwayarsu ko ba za su ba su komai ba su rika daukar nauyin karatun ’ya’yansu har don su ma su zamo wadansu wata rana domin ilmi shi ne ginshikin zaman duniya.

A karshe sabon Sarkin Makafin ya yi alkawarin kwatanta adalci tare da tafiya da duk wanda ke karkashinsa ba tare da nuna wariya a tsakanin Musulmi ko Kirista ba tunda a cewarsa, ’yan uwansa makafi Kiristoci da ke karkashin masarautar musamman sun kai masa ziyara tare da yi masa mubaya’a.