✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An naushe dan damben boksin ya mutu

Maxim Dadashev, dan damben boksin dan asalin Rasha ya mutu jim kadan bayan ya sha haushi a wajen Puerto Rico’s Subreil Matias a damden da…

Maxim Dadashev, dan damben boksin dan asalin Rasha ya mutu jim kadan bayan ya sha haushi a wajen Puerto Rico’s Subreil Matias a damden da suka fafata a filin wasa na MGM National Harbor a tsaunin Oxton Hill da ke Maryland na Amurka. Al’amarin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta wuce.

Wata sanarwa da kocinsa Buddy MaGirt ya fitar ta ce “Muna bakin cikin shaida muku cewa, dan damben boksin, dan asalin Rasha Maxim Dadashev ya rasu a wani asibiti a Amurka bayan ya samu raunuka a wasan da suka yi da takwaransa Puerto Rico’s a ranar Juma’ar da ta wuce.  An garzaya da shi ne bayan ya samu raunuka saboda naushi, kuma a can ne rai ya yi halinsa.”

Jama’a da dama masu sha’awar wasan damben boksin sun kadu sosai da suka samu labarin rasuwarsa.  Sun yi ta rububin aika sakonnin ta’aziyyarsu ga kocin da kuma iyalan mamacin.

Marigayi Dadashev ya rasu yana da shekara 28. Ya fafata a wasannin damben boksin sau 14 inda ya samu nasara a wasanni 13 yayin da aka doke shi a wasa dayan da ya yi ajalinsa.