✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nemi gwamnati ta sake gina kasuwar kayan gargajiya ta Abuja

An yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta yi gaggawar sake gina shagunan da suka kone a kasuwar sayar da kayan gargajiya ta Abuja, sakamakon gobarar…

An yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta yi gaggawar sake gina shagunan da suka kone a kasuwar sayar da kayan gargajiya ta Abuja, sakamakon gobarar da ta auku a kasuwar a makon da ya gabata.

Shugaban ’yan kasuwar, Kanayo Chukwumezie ne ya yi kiran a yau Laraba yayin da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya kai musu ziyara don jajanta musu gobarar ta da auku a kasuwar a kwanan nan.

Kanayo ya ce “mun tafka asara mai yawa, shaguna 36 ne suka kone sannan mun yi asarar kimanin Naira miliyan 400 zuwa 500. Saboda haka muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta yi gaggawar sake gina kasuwar nan tare da biyan diyya ga wadanda shagunansu suka kone, don su ci gaba da gudanar da kasuwancinsu,” inji shi.

Ya bayyana cewa Sanata Rabi’u Kwankwaso shi ne dan siyasa na farko da ya je har kasuwar ya jajanta masu. Saboda haka sai ya yi kira ga sauran jama’a da masu hannu da shuni da kuma gwamnati su taimaka masu don murmurewa daga bala’in da ya auka masu.

Shugaban wanda ya yi zargin makarkashiya cikin tashin gobarar, ya bayar da tabbacin cewa sun dauki matakan da suka kamata don kare sake aukuwar lamarin nan gaba.

Da yake jawabi yayin da yakai ziyara kasuwar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi alkawarin daukar matakan da suka kamata don ganin cewa gwamnati ta yi abin da ya kamata ga ’yan kasuwar.