✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nemi masu juna biyu su rika zuwa gwajin cutar kanjamau

Uwargidan Shugaban Karamar Hukumar Jama’a, Misis Salamatu Peter Aberik ta shawarci ma’aurata a yankin su taimaka wa yunkurin da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i…

Uwargidan Shugaban Karamar Hukumar Jama’a, Misis Salamatu Peter Aberik ta shawarci ma’aurata a yankin su taimaka wa yunkurin da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ke yi na ganin bayan cutar kanjamau a fadin jihar musamman wanda uwa mai shayarwa kan sanya wa jaririnta, ta hanyar zuwa gwaje-gwaje da kuma karbar shawarwari da ake gudanarwa kyauta.

Malama Salamatu Aberik ta yi wannan kira ne a yayin wata ziyara da ta kawi Cibiyar Kula da Lafiya a Matakin Farko (PHC) da ke Gundumar Kafanchan (A) don gane wa idonta yadda aikin wayar da kai ga mata masu ciki da masu shayarwa da ake yi game da cutar kanjamau.

Yayin da ta yaba amsa kiran matan da suka fito da yawa,  ta ce aikin gwaje-gwajen ciwon kanjamau (HIB/AIDS) da ake yi da bayar da shawarwari da magunguna ana yi ne kyauta a kanana da manyan asibitocin gwamnati a fadin Jihar Kaduna.

Sai ta nanata muhimmancin bai wa yara zallar nonon uwa don samun koshin lafiya da kuma shawartar masu dauke da juna biyu su tabbatar suna zuwa awon ciki tare da zuwa asibiti idan sun ji alamun haihuwa don guje wa wasu matsaloli.Ta ce su rika yawan kai jariransu asibiti don samun dukkan alluran rigakafin da ake rubuta musu bayan haihuwa.

Da take gabatar da jawabi, Babbar Jami’ar Yaki da Yaduwar Cutar Kanjamau daga uwa zuwa ga jariri na asibitin, Misis Paulina Bako ta jinjina wa Uwargidan Shugaban Karamar Hukumar ce bisa kokarin da take yi wajen ba su kwarin gwiwa, inda ta bayyana ta a matsayin uwa abar koyi.

Sai ta yaba wa Shugaban Karamar Hukumar da taimakawar da yake yi ga asibitin ta hanyar yin gyare-gyare da kwaskwarima da kuma samar musu da magunguna da sauran kayan aiki, inda ta roki jama’a su rungumi wannan tallafin ta hanyar zuwa asibitin.