✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nemi sarakuna su rika kafa kwamitin sulhunta Fulani da manoma

Shugaban kungiyar Miyetti-Allah na kasa, Alhaji Muhammadu Kiruwa Ardon Zuru ya nemi sarakunan kasar nan da su rika kafa kwamitoci da za su kawo karshen…

Shugaban kungiyar Miyetti-Allah na kasa, Alhaji Muhammadu Kiruwa Ardon Zuru ya nemi sarakunan kasar nan da su rika kafa kwamitoci da za su kawo karshen rashin jituwa da take tasowa a tsakanin al’ummar Fulani makiyaya da manoma, kamar yadda masarautar Argungu ta yi.

Alhaji Muhammadu Kiruwa ya bayyana haka ne a lokacin da ya kaiwa Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Muhammadu Sama’ila Mera (CON) ziyarar ban girma a fadarsa.

Shugaban kungiyar ya ci gaba da cewa, ta hanyar da masarautar Argungu ta bi ta kafa kwamitoci domin gano matsalolin dake faruwa tsakanin Fulani da manoma ce mafita, domin asan hanyoyin da za a magance su a cikin ruwan sanyi.

Alhaji Muhammadu Kiruwa ya ce idan ana son irin wadannan kwamitoci su yi tasiri, to ya kamata a kafa su a kowace masarauta a kasar nan ya ce idan aka yi haka za a sami hanyar da za a magance matsalar.

Ya yi amfani da wannan dama inda ya yi kira ga sarakuna da hakimansu da su ci gaba da ba Fulani makiyaya goyon baya da kuma ba su hakkinsu kamar yadda suke ba manoma domin su ma talakan su ne kamar yadda manoma suke a gare su. 

Da karshe ya yi kira da Fulani makiyaya da su kaucewa shiga gonakin manoma domin kawo zaman lafiya da cigaban kasa, su kuma rika bin doka da oda da girmama sarakuna a duk inda suke. Da yake maida jawabi, Sarkin Kabin Argungu ya gode wa shugaban kungiyar da tawagarsa bisa wannan ziyarar ta ban girma da suka kawo masa a fadar tasa.