✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nemi ya fito takarar gwamna ko a maka shi a kotu

Wasu kungiyoyi masu kishin Jihar Sakkwato, sun yi barazanar kai karar tsohon Shugaban Majalisar Dokokin jihar kuma Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Gwadabawa…

Wasu kungiyoyi masu kishin Jihar Sakkwato, sun yi barazanar kai karar tsohon Shugaban Majalisar Dokokin jihar kuma Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Gwadabawa da Illela, Abdullahi Balarabe Salame, muddin ya ki fitowa neman kujerar Gwamnan jihar a 2023.

A taron manema labarin da kungiyoyin suka kira, shugaban kungiyar Peace and Justice Network, Yusuf Jibo Gwashi, ya ce muddin Salame ya yi watsi da buktar to za su dauki matakin shari’a don su tabbatar ya yi takarar.

“Mun gamsu da gogewarsa da halayensa na gari da buri da kudirinsa na ciyar da Jihar Sakkwato gaba.

“Jiharmu na bukatar mutum wanda aka gwada shi kuma aka ga rikon amanarsa kuma zai iya ciyar da jihar gaba.

“Irin cigaban da ya samar a mazabar da yake wakilta a karkashin jam’iyyar APC ya isa zama hujja a kan hakan”, inji shi.

Ya kara da cewar “wasu kungiyoyin masu son ci gaba ne da ba su da alaka da jam’iyyar APC, kuma sun tabbatar Salame ya cancanta duba da yadda ya jagoranci Majalisar Dokokin Jihar da kuma yadda ya rike jihar a matsayin mukaddashin gwamna.

“Salame ya samu nasarori a mukaman da ya rike, saboda haka muke ganin dacewar ya tsaya takarar Gwamnan Sakkwato a jam’iyyar APC”, kamar yadda ya bayyaa.