✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An raba auren shekara 18 saboda kaurace wa kwanciyar iyali

Ta daina bari na kusance ta tun bayan haihuwar dan mu na karshe shekaru bakwai da suka gabata.

A ranar Juma’ar da ta gabata ce wata Kotun al’adu dake zamanta a yankin Mapo na birnin Ibadan a jihar Oyo, ta katse igiyar auren shekara 18 tsakanin wani malami, Juel Olutunji da matarsa, Blessing saboda ba ta bari ya kusance ta.

Yayin zartar da hukuncin, Mai Shari’a Ademola Odunade, ya ce an raba auren saboda a samu zaman lafiya tsakanin ma’auratan biyu.

Aminiya ta ruwaito cewa, Kotun ta bai wa Olutunji ikon rike ’ya’yansu biyu na fari yayin da kuma aka bar wa Blessing yaro daya na goye.

Alkali Odunade ya kuma umarci Olutunji da ya rika biyan Blessing Naira dubu biyar duk wata a matsayin kudin dawainiya da yaro da aka bar ta mata riko.

Tun da fari dai Olutunji ya shaida wa kotun cewa kasancewarsa tare da Blessing bay a da kwanciyar hankali domin ta jefa shi cikin dimuwa kuma bai saboda ta fitini rayuwarsa.

Ya ce, “tun bayan haihuwarmu ta farko bayan auren mu a shekarar 2002, Blessing ta sauya halayenta.”

“Blessing ta daina bari na kusance ta tun bayan haihuwar dan mu na karshe shekaru bakwai da suka gabata.”

“A karshe dai ta dauki duk wani mataki na hana ni ganin ’ya’yana,” inji Olatunji.