✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rada wa jikan Yarima Charles sunan George

An rada wa jaririn gidan sarautar Birtaniya sunan George Aledander Loui, don haka fada ta bayar da sanarwar za a rika kiransa da sunan Mai…

Yarima Williams da Gimbiya Kate, tare da jaririnsu, George Alexander LouisAn rada wa jaririn gidan sarautar Birtaniya sunan George Aledander Loui, don haka fada ta bayar da sanarwar za a rika kiransa da sunan Mai martaba Yarima George na Cambridge. Tuni ’yan caca suka yi kokarin cankar sunan jariri, inda aka raba zaben sunan tsakanin George da James.
An kawata dandalin Trafalgar da fitilu iri-iri, don a nuna cewa an haifi namiji a gidan sarauta ga Yarima William da Gimbiya Catherine. Wannan haihuwa dai an yi ta ne ranar Litinin, inda aka samar wa gidan sarautar Birtaniya magaji, wato sarkin wata rana, kamar yadda aka yi hasashe a daukacin fadin duniya, a cewar fadar Kensington.
Yarima Williams ya kasance a gefen gadon matarsa lokacin da take nakuda, don yana hutunsa na shekara, kuma za a ba shi hutun haihuwa na makonni biyu, a wurin aikinsa na rundunar sojan saman Royal Air da ke Birtaniya; wannan runduna na da alhakin bincike da ceton matukan jiragen sama da suka shiga wani hali.
Uwa da dan na cikin koshin lafiya, kuma sun kasance a cikin asibiti na tsawon kwana daya, kamar yadda aka bayyana cewa, “sarauniya na cike da farin ciki.”
An dai yi wannan haihuwa sabanin yadda aka saba. Taron masoyan wadannan ma’aurata sai karuwa yake. Domin ba a taba ganin irinsa ba, tun bayan da mahaifiyar William Diana ta mutu a wani hadarin mota a kasar Faransa cikin shekarar 1997. A wajen bikin auren Kate Middleton da William, an yi gagarumin taro cikin watan Afrilun 2011.
Mafi yawan ’yan caca sun karfafa hasashensu da cankar mace za a haifa, bayan da suka ji Kate ta ce ba su san jinsin jaririn ba.
Ganin cewa jaririn da aka haifa namiji ne, babu bukatar a sake duba dokokin gadon sarauta har 16, wadanda ke nuni da cewa kanen mace ba zai iya shiga gabanta ba (a jerin magadan karagar mulki).
Wadannan ma’aurata ’yan gidan sarauta, sun shiga asibitin ne ta baya da kimanin karfe shida na yammacin ranar Litinin, don kauce wa manema labarai daga kafofin yada labarai na duniya, wadanda suka yi sansani har na tsawon makonni uku a kofar asibitin.
Wannan jaririn Yarima an haife shi ne a bangaren asibitin da daukacin kafafen yada labarai suka ruwaito al’amarin da ya auku  shekarar 1982, lokacinm da matar Charles ta farko, uwargida Diana ta haihu.
Masu tsananin kishi da kaunar jama’ar gidan sarautar Ingila sun taru a gaban asibitin, inda suka cika da doki. “Ina cike da murna,” a cewar John Lughrey, wanda ya kwana a kofar asibitin har tsawon mako guda inda ya lullube jikinsa da tutar Birtaniya.
Wannan jariri da aka haifa shi ne tattaba-kunnen sauraniya na uku, kuma jikan Yarima Charles na farko.
An ga Sarauniya ta fito daga fadar Buckingham da ke gidan sarauta a Windsor, a wajen birnin, cikin tsakar rana, amma sauran ’yan gidan sarauta sun ci gaba da harkokinsu na rayuwa.
Shi kuwa Yarima Charles, wanda shi ne magajin Sarauniyar Ingila, ya tafi garin York ne da ke Arewacin Ingila, inda ya iske cincirindon mutane suna ta ihu da karajin taya shi murna, “Barka muna murna!” Sai ya yi murmushi, sannan ya ce musu: “ko kun san wani abu da ni ban sani ba?”
Yarima Charles, wanda a halin yanzu shekarunsa 65, ya yi barkwanci, inda ya ce: “Na yi matukar godiya da farin ciki duk da cewa na yi lakaki wajen zama kaka.”
Firayiministan Birtaniya, Dabid Cameron ya aike da sakon fatan alheri ga ma’aurata, a daidai lokacin da daukacin kasar ake cike da murna.
An sanar da labarin laulayin Gimbiya Kate a watan Disambar bara, bayan da aka kwantar da ita a asibitin saboda fama da laulayin juna biyu a kowace safiya.
kwararrun masana kan kula da lafiyar mai juna biyu da ke aiki a fadar Sarauniya, Alan Farthing da Marcus Setchell ne suka tarairayi Gimbiya Kate har ta haifi dan nata.
A wani dandamali da ke kallon kofar shiga asibitin, kimanin masu gabatar da shirye-shirye 30 ne suka yi layi, don aikewa da labaran al’amuran da ke wakana kai-tsaye. Su kuwa masu daukar hoto da ’yan jarida a wuri guda suka tare.