✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rada wa kwallon da za a yi amfani da ita a gasar cin kofin duniya suna

Hukumar kula da shirya wasan kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta fitar da samfurin kwallon da za a yi amfani da ita a gasar cin…

Hukumar kula da shirya wasan kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta fitar da samfurin kwallon da za a yi amfani da ita a gasar cin kofin duniya a shekara mai zuwa a Brazil suna.
kwallon wacce ke dauke da kaloli masu daukar ido an sanya mata sunan “Brazuca” ne bayan kimanin mutane miliyan daya sun kada kuri’arsu wajen tantance sunan da aka rada wa kwallon.
Sunan ya yi daidai ne da al’adun mafi rinjayen al’ummar kasar kuma tuni ya samu amincewar Hukumar.
An gayyaci jiga-jigan ’yan kwallo su kimanin 600 daga sassan duniya a bikin radawa kwallon suna.
Daga cikin ’yan kwallon da suka halarci bikin sun hada da Lionel Messi da Iker Casillas da Bastian Schweinteiger da kuma tsohon dan kwallon Faransa Zinedine Zidane.
Tuni ’yan kwallon suka amince da kala da kuma sunan da aka radawa kwallon.