✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rage farashin man fetur daga Naira 145 zuwa 126

Gwamnatin tarayyar Najerya ta amince da rage farashin man fetur daga Naira 145 zuwa Naira 126. An sanar da rage farashin man fetur din bayan…

Gwamnatin tarayyar Najerya ta amince da rage farashin man fetur daga Naira 145 zuwa Naira 126.

An sanar da rage farashin man fetur din bayan bayanin da karamin Ministan Man Fetur Timipre Sylva, ya gabatar yayin zaman Taron Majalisar Zartarwa (FEC) da aka sabayi yau duk mako, wanda shugaba Muhammadu Buhari  ya jagoranta yau Laraba.

Rahotan ya kara da cewa, an rage farashin ne sakamakon faduwar farashin danyan mai daga dalar Amurka $60 zuwa tsakanin farashin dala $29 da $30.

A yanzu haka Gwamnatin tarayya za ta fara fitar da farashin ne daga sauyin farashin danyan man da ake sayarwa a kasuwannin duniya, hakan zai shafi yanayin farashin man fetur na Najeriya idan an samu sauyi.