✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘An rage wa Yariman Saudiyya karfin iko’

Rahotanni daga Saudiyya na nuna cewa Yariman Saudiyya Mohammad bin Salman bai halarci wasu manyan tarurrukan manyan ministoci da jakadu da aka gudanar a kasar…

Rahotanni daga Saudiyya na nuna cewa Yariman Saudiyya Mohammad bin Salman bai halarci wasu manyan tarurrukan manyan ministoci da jakadu da aka gudanar a kasar a mako biyu da suka gabata ba, kuma ana tsamnmanin an rage masa karfin iko ne a kan tattalin arziki, kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

Takaitawa ko rage karfin ikon Yariman ana tsammanin ya taso ne bayan wani taron da manyan ministocin kasar da Sarki Salman suka yi.

Duk da cewa har yanzu ba a bayyana lamarin a fili ba, jaridar The Guardian ta ruwaito daga majiyarta cewa wani daga manyan na kusa da Sarki Salman, Musaed al-Aiban, wanda ya yi karatu a Harbard wanda kuma kwanan nan aka nada mai ba da shawara kan tsaro, shi ne zai ci gaba da lura bangaren harkokin kasuwancin kasar a kasashen waje a madadin Sarkin

Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Washington ya ki amsa tambayoyin da The Guardina a kan batun.