✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rantsar da shugabannin Kungiyar Kayan Marmari ta Zuba

An rantsar da sababbin shugabannin Kungiyar Masu Kayan Marmari da ke  Zuba  a Karamar Hukunar Gwagwalada a Abuja. Sababbin shugabannin da aka sun hada da…

An rantsar da sababbin shugabannin Kungiyar Masu Kayan Marmari da ke  Zuba  a Karamar Hukunar Gwagwalada a Abuja.

Sababbin shugabannin da aka sun hada da Alhaji Mohammed Ibrahim Talba a matsayin Shugaba. Sai kuma Yusuf Nakande,  Mataimakin Shugaba. Kabiru Alfa, Magatakarda da Sadik Isma’il, Ma’ajin Kungiyar. Sai Hussaini Salihu, a Sakataren Kudi na kungiyar.

A yayin da yake jawabi a wurin taron ranar Lahadin da  gabata, Shugaban Karamar Hukumar Gwagwalada, Alhaji Adamu Mustapha, ya ce yana cike da farin cikin ganin cewa an yi zaben cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali ba tare da tashin hankali ba. Sai ya yi kira ga shugabannin kungiyar su tabbatar cewa an yi zaman lafiya tare da wadanda suka yi takara da su ba su samu nasara ba. Ya ce da zaman lafiya da hadin kai ne kawai kasuwar za ta bunkasa; don haka ya  bukaci shugabannin su tabatar cewa an samu zaman lafiya da  hadin kai a tsakaninsu.

Ya jawo hankalinsu kan su cire hannunsu a harkokin siyasa domin yin haka ne zai sa a samu ci gaba a wannan kasuwar.

A jawabin sabon Shugaban Kungiyar Kayan Marmarin, Alhaji Mohammed Ibrahim Talba, ya  gode ea mambobin kungiyar da suka ba su goyon baya wajen zabarsu don kula da harkar kasuwar.

Yana kuma gode wa Mai martaba Agoran Zuba, Alhaji Mohammed Bello Umar da majalisarsa kan goyon baya da ya ba kungiyar domin ganin an yi zaben lafiya.

Alhaji Talba ya yi alkawarin cewa zai tabbatar da cewa ya hada kai da sauran shugabanni wajen ganin an samu zaman lafiya da ci gaban kasuwar.

Ya ce kungiyar za ta zauna nan bada jimawa ba domin duba yadda za su tsara taswirar da za su tafiyar da harkokin kungiyar.