✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rataye mutum 21 saboda aikata ta’addanci

Shugaban Kasar ne ya ba da lamuni a kan hukuncin da aka zartar a ranar Litinin.

Kasar Iraki a ranar Litinin ta kashe fursunoni 21 a gidan yarin Nasiriya da ke Kudancin Kasar bayan an yanke musu hukunci na ta’addanci kamar yadda jami’an lafiya da na tsaro suka tabbatar.

Fursunonin 21 wanda dukkaninsu maza ne sun fito ne daga larduna daban-daban na kasar wanda kuma hukuncin kisa ya hau kansu a karkashin Dokar Ta’addanci ta 2005, sai dai babu cikakken bayani kan takamaiman laifin da suka aikata.

An rataye su a kurkukun Nasiriyah da ke lardin Dhi Qhar, wanda shi kadai ne gidan yarin da Iraki ke zartar da manyan hukunci a cikinsa.

Tun bayan da ta ayyana karya kungiyar IS a karshen shekarar 2017, Iraki ya yanke wa daruruwan ’yan kasarta hukuncin kisa sakamakon kasancewarsu da kungiyar da ta daura damarar ta’addanci da sunan Jihadi.

Sai dai kadan ne daga cikin hukuncin aka zartar a yayin da ya zama wajibi sai an samu amince wa daga Shugaban Kasar na yanzu, Barham Saleh.

Majiyoyi daga jami’an tsaro sun tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Shugaba Saleh ne ya ba da lamuni a kan hukuncin da aka zartar a ranar Litinin.

Kotunan Iraki sun kuma yi shari’ar wasu ’yan kasashen ketare da dama kan zargin kasancewarsu mambobin kungiyar IS, inda aka yanke wa wasu ’yan kasar Faransa 11 da kuma wani dan kasar Belgium daya hukuncin kisa.

Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International, ta sanya kasar Iraki a mataki na biyar cikin jerin kasashen duniya da suke zartar da hukuncin kisa, inda ko a shekarar 2019 aka samu kasar ta zartar da hukuncin kan mutum 100.

Amnesty da wasu kungiyoyi masu rajin kare hakkin bil Adama sun yi tir da tsarin doka na kasar Iraki, inda suka riki cewa ana gaggauta zartar da hukunci ba tare da bai wa wanda ake tuhuma damar kare kansu ba ta hanyar da ta dace.

Sun kuma yi Allah wadai dangane da yadda ake azabtar da fursononi a gidajen yarin kasar.