✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An raunata shugaba da wasu wakilai a dambarwar Majalisar Jiha Ribas

Yunkurin da wasu ’yan majalisa biyar suka yi domin tsige shugaban Majalisar Dokokin Jihar Ribas Otelemaba Dan Amachere a ranar Talatar da ta gabata bai…

Cif Rotimi Amaechi Gwamnan Jihar RibasYunkurin da wasu ’yan majalisa biyar suka yi domin tsige shugaban Majalisar Dokokin Jihar Ribas Otelemaba Dan Amachere a ranar Talatar da ta gabata bai yi nasara ba, sai dai shugaban da wasu ’yan majalisar da dama sun samu raunuka a fafatawar da ta auku a lokacin.
Bayanai sun nuna cewa wani dan majalisar ya jagoranci wasu ’yan daba zuwa majalisar wadda suka mamaye ta inda suka shiga dukan mutane ciki har da shugabanta da shugaban masu rinjaye Chidi Lloyds wanda ya sha dukan kawo wuka da ya kai shi ga kwanciya a asibiti.
Ana zargin ’yan majalisar biyar wadanda aka dakatar da su da ke samun daurin gindin Minista a Ma’aikatar Ilimi, Barista Nyesom Wike a karkashin jagorancin Felid Obuah wanda bai cikin dakatattun ne suke kokarin kwace shugabancin majalisar.
Gwamnan Jihar Ribas Rotimi Amaechi wanda ya ziyarci majalisar lokacin da ya samu labarin dambarwar da ke gudana a cikinta, ziyarar tasa ta so kazanta lamarin. Wata majiya ta ce ana zargin wani dan majalisa da ba umarnin a harbi Gwamnan lokacin da ya hango shi, wannan ya sa Gwamnan ya tsallake rijiya da baya inda “jami’an tsaronsa suka yi maza suka kewaye shi suka yi gaba da shi,” inji majiyar.
Bayan da shugaban majalisar ya tsallake wannan yunkuri na tsige shi da kuma yi masa maganin raunin da ya samu ya koma majalisar inda shi da ’yan majalisa 23 suka zauna suka tattauna wani kudiri da gwamnatin jihar ta gabatar ga majalisar, sai dai a wannan karo ’yan dabar sun auka wa Mataimakin Gwamnan Jihar Injiniya Tele Ikuru da misalin karfe 12:26 na rana.
Mukaddashin Sakataren Watsa Labarai na Mataimakin Gwamnan Godswill Jumbo,  ya fadi a wata sanarwa cewa mai gidan nasa ya je majalisar ce domin gabatar gyare-gyare ga kasafin kudin jihar na bana a madadin Gwamnan Jihar Chibuike Rotimi Amaechi.
Ya ce a kan hanyarsa ta mika kasafin ne ’yan dabar da suka cika harabar majalisar suna wake-waken yaki don nuna goyon baya ga wani dan majalisa mai suna Ebans Bapakaye Bipi, sai suka auka wa Mataimakin Gwamnan lokacin da suka hango shi.
Ya ce sun lalata motarsa ta aiki da sauran motocin da suke cikin ayarinsa, kuma sun kai farmaki ga ayarin ta yadda wasu suka gudu a kafa don kauce wa faruwar mugun abu.An zargi dan majalisa Ebans da duka da cin zarafin mai daukar hoto na gidan talabijin na Channels Telebision inda ya kwace masa kyamarar daukar hoton bidiyo.