✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe cibiyoyin da ake ‘zubar da ciki’ a Nijar

Mahukunta a Jamhuriyyar Nijar sun bayar da umarnin a rufe cibiyoyi biyu na wata Hukumar Agaji ta Birtaniya, Marie Stopes International, inda suka ce suna…

Mahukunta a Jamhuriyyar Nijar sun bayar da umarnin a rufe cibiyoyi biyu na wata Hukumar Agaji ta Birtaniya, Marie Stopes International, inda suka ce suna ayyukan zubar da ciki ba bisa ka’ida ba.

Gidan rediyon BBC ya ruwaito daga Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa (AFP), cewa Ma’aikatar Lafiya ta kasar ta ce an dauki wannan mataki ne saboda bukatar hakan ta taso.

A shekarar 2006 ce, gwamnatin Nijar ta zartar da dokar cewa ba za a zubar da cikin kowace mace ba, sai in rayuwarta tana cikin hadari sakamakon cikin da take dauke da shi.

Har zuwa yanzu dai kungiyar ba ta ce uffan ba a kan batun.

Kiyasi ya nuna cewa mace daya a Nijar na haihuwar akalla ’ya’ya bakwai a tsawon rayuwarta,  wanda shi ne adadi mafi yawa a duniya.

A farkon wannan wata ne Kenya, wacce take da tsauraran dokoki kan zubar da ciki ta dakatar da ayyukan zubar da ciki da kungiyar Marie Stopes International ke gudanarwa.