✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe shagunan ‘Yan Najeriya 50 a Ghana

Kungiyar masu sana’ar kayan wutar lantarki ta kasar Ghana, ta rufe shagunan baki ‘yan kasashen waje da ke kasuwanci a kasar, wadanda suka taka dokar…

Kungiyar masu sana’ar kayan wutar lantarki ta kasar Ghana, ta rufe shagunan baki ‘yan kasashen waje da ke kasuwanci a kasar, wadanda suka taka dokar da aka gindaya wa ‘yan kasuwar. A kalla shagunan ‘yan Najeriya 50 aka rufe a yankin Opera Square da ke Accra ta Tsakiya.

‘Yan kasuwar na Ghana sun ce ‘yan kasashen waje musamman ‘yan Najeriya na gudanar da harkokin kasuwanci ba bisa ka’ida ba.

A makon da ya gabata ne kungiyar ‘yan kasuwar suka sanar da ‘yan kasashen waje da ke kasuwanci su kauracewa inda shagunan su suke kafin ranar 4 ga Nuwamba 2019.

Kakakin kungiyar Samuel Addo, ne ya sanar da hakan ya bayyanna cewa, an wari inda rumfunan ‘yan Najeriyan suke ne don ‘yan kasar Ghana su yi harkokin kasuwancin su masu karafin karfi kamar yadda dokar ta tanadar.