✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rusa Hukumar jin dadin alhazai ta Katsina

A ranar Juma’ar nan ne Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya rushe hukumar gudanarwa ta ma’aikatar jin dadin alhazai ta jahar kwanaki kadan bayan…

A ranar Juma’ar nan ne Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya rushe hukumar gudanarwa ta ma’aikatar jin dadin alhazai ta jahar kwanaki kadan bayan kammala aikin hajji na wannan shekara ta 2019.

Gwamna Masari ya umarci Babban Daraktan Hukumar da ya miqa ragamar mulkin hukumar ga wanda ya fi kowa mukami daga cikin ma’aikatar hukumar. Wannan matakin ba zata da Gwamnan ya dauka kamar yadda wata majiya ta ruwaito baya rasa nasaba da irin korafe-korafen da aka rika samu akan wasu matsalolin da ba’a baiyana ba.