✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace mai jego da mutum 5 a Kaduna

Acikin dare ranar Talatar da ta gabata wadansu ’yan bindiga suka sace wata mai jego da wadansu mutum biyar a Unguwar Dan Mani da ke…

Acikin dare ranar Talatar da ta gabata wadansu ’yan bindiga suka sace wata mai jego da wadansu mutum biyar a Unguwar Dan Mani da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

’Yan bindigar sun yi wa unguwar dirar mikiya ce da misalin karfi 3:15 na dare inda suka rika bi gida-gida suna daukar mutane.

Daya daga cikin masu unguwannin yankin da bai so a ambaci sunansa ba, ya tabbatar wa Aminiya aukuwar lamarin inda ya ce sace mutanen ya jefa tsoro a zukatan jama’a.

“Lamarin ya auku ne da misalin karfe 3:15 na dare, inda muka rika jin harbi. Kusan dukkanmu da ke unguwar ba mu yi barci ba. Yanzu haka sun sace wata mata mai jego, mijinta Ghali ya tsira. Sun sace Gambo da Bukar Mandara. Akalla dai mutum shida muka tabbatar da  sun sace,” inji shi.

Ya yi kira ga gwamnati ta kai masu dauki domin a cewarsa wannan ne karo na farko da masu garkuwa da mutane suka sace mutane a unguwar.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo ya ce yana cikin wani taro a lokacin da wakilinmu ya kira shi ta waya, don haka zai kira idan sun kammala amma dai bai kira ba har zuwa hada rahoton.