Da Dumi Dumi

An sace motar wanda ya shiga fashi a shago

An sace motar wani barawo da ya sha kwayoyin maye, lokacin da ya shiga cikin wani shago yana yin fashi a gefan hanya. A ranar Lahadi n da ta gabata ce da misalin karfe 6:00 na safe wani mutum  mai suna William Kelley, ya ajiye motarsa kirar ‘1992 Cheby pickup’ a birnin Washington da ke Amurka bayan ya kwana a mashaya.

A cewar William, ya bar mabudin motar a kan kujerar motar kafin a sace ta.

A yayin da William yake cikin shagon yana  fashi, sai wani mutum ya taho a kan babur ya dauke mabudin motar daga bisani ya dauke motar.

Bayan da William, ya fito daga cikin shagon da ya yi fashin sai ya nemi motarsa ya rasa daga nan ne sai ya kira ’yan sanda don neman taimakonsu  cewa an yi masa sata. Sai dai kafin William ya nemi agajin ’yan sanda sun riga sun ba da umarnin a tsare shi.

A lokacin da  ’yan sandan suka tsare William, mai shekara 42 ya ce ya shiga shagon sayar da barasa ce don ya biya bukata a ban-daki, amma sai kyamarar bidiyon CCTB ta nuna  William, yana yi wa jama’a fashi a cikin shagon.

ADVERTISEMENT

“An sace motar William ne lokacin shi ma yake cikin shago yake satar kaya,” inji ’yan sandan.

’Yan sandan sun tsare William, kuma ba a kammala bincike don gano inda aka kai motar ba, sai dai ’yan sandan sun sanar da jama’a cigiya kan satar motar William.

 

Share