✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace mutum shida an kashe ’yan sanda 2 a Adamawa

Rohotonni sun ce wadansu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mutum shida tare da kashe ’yan sanda biyu a hanyar Gyella da ke Karamar Hukumar…

Rohotonni sun ce wadansu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mutum shida tare da kashe ’yan sanda biyu a hanyar Gyella da ke Karamar Hukumar Mubi ta Kudu a Jihar Adamawa.

Kamar yadda Aminiya ta samu labari, lamarin ya auku ne da misalin karfe bakwai na yamma zuwa takwas a ranar Litinin da ta gabata a yayin da ’yan sandan ke dawowa daga hedkwatarsu ta Mubi inda suka damka wadansu da ake zargi da laifi.

Rahotanni sun ce mutanen Karamar Hukumar Mubi sun sanar da ’yan sanda game da wadansu mutane da ake zargin ’yan Boko Haram ne, musamman ganin yadda suke sayen abinci mai yawa a kasuwarsu.

Hakan ya sanya ’yan sandan suka shiga bincike har suka yi nasarar kama wadansu kuma suka mika su a hedkwatarsu ta Mubi.

Bayan sun mika su ne a hanyarsu ta dawowa suka yi kicibis da ’yan bindiga inda suka kashe ’yan sanda biyu tare da yin garkuwa da wadansu matafiya shida.

A makon jiya ne aka yi garkuwa da wani babban jami’in ’yan sanda wato DPO a Jihar Adamawa mai suna Ahijo Muhammed da wani dan kasuwa Muhammadu Mbilla wadanda har yanzu ba a san inda suke ba.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Adamawa, Suleiman Nguroje ya ce bai da masaniya kan faruwar lamarin, amma ya ce za su gudanar da binciki.