✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace shanu fiye da 300 a Filato

A farkon wannan makon ne wasu barayi suka yi awon gaba da shanu fiye da 300 a yankin karamar Hukumar Riyom da ke Jihar Filato.…

A farkon wannan makon ne wasu barayi suka yi awon gaba da shanu fiye da 300 a yankin karamar Hukumar Riyom da ke Jihar Filato. Wani jami’in kungiyar Miyetti Allah, Malam Muhammad Abdullahi ne ya bayyana haka ga manema labarai, inda ya ce sun yi imanin barayin sun fito ne daga karamar Hukumar Bassa ta jihar.

Ya kuma kara da cewa, barayin sun far wa yaransu makiyaya a kauyen Gidan Ado, inda suka fatattake su suka kora su. Daga nan ne sai yaran suka gudu suka bar dabbobin, kamar yadda ya ce.

Haka kuma ya ce “maharan sun tafi da wadansu dabbobin kimanin 150. Ya ce abin bai tsaya a nan ba, domin daga bisani sun sake dawowa wani kauye a yankin, suka kara sace shanu kimanin 200.”

Kakakin rundunar ‘yan sanda a Jihar Filato, ASP Tyopeb Mathias Terna ya tabbatar da faruwar lamarin. Sai dai ya ce jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ‘yan sanda suna nan suna aiki don tabbatar da cewa sun kwato shanun tare kuma da cafke barayin.

Kodayake wani makiyayin da satar ta shafa ya ce jami’an tsaro sun shaida musu cewa sun gano wasu matattun shanun da ake zaton wadanda aka sacen ne tun farko, kimanin su 56.

Hakazalika ya ce an samu wadansu fiye da guda 20 da aka yi musu munanan raunuka da ba za su iya tafiya ba. Kuma ya ce sauran shanun ba a gansu ba. Amma ya ce akwai ragowa da aka kwato a hannun barayin wadanda suke hannun jami’an tsaro a halin yanzu.

A baya dai jihar ta yi fama da rikice-rikice tsakanin makiyaya da al’ummomin yankuna daban-daban, wadanda galibinsu manoma ne. Sai dai jihar ta samu kwanciyar hankali fiye da shekaru biyu da suka wuce. Duk da cewa a baya-bayan nan matsalar rikice-rikicen ta sake yin kamari a jihohi masu makwabtanta kamarsu Benuwai da Taraba da kuma Adamawa.