✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace tsohon dan Majalisar Wakilai a Jihar Bauchi

Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun sace tsohon dan Majalisar Wakilai daga mazabar Darazo da Alhaji Sama’ila Ilali…

Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun sace tsohon dan Majalisar Wakilai daga mazabar Darazo da Alhaji Sama’ila Ilali a gidansa da ke garin Darazo a ranar Lahadi da ta gabata da misalin karfe biyu na dare.
Alhaji Sama’ila mai shekara 65 ya kasance dan Majalisar Wakilai a shekarar 2007 zuwa 2011 kuma a yanzu yana kokarin fitowar takarar Sanatan Bauchi ta Tsakiya ne a karkashin Jam’iyyar APC.
Har zuwa hada wannan rahoto babu labarinsa kuma babu wata bukata daga wadanda suka sace shi ga iyalansa ko wata hukuma.
Makwabcinsa wanda tsohon dan Majalisar Wakilai ne, Alhaji Kawu Labaran ya ce sun ji karnuka na kuka lokacin da aka zo tafiya da shi, amma ba su san abin da ke faruwa ba sai da safe, kuma jama’a sun ce sun ga mutane suna atisayen a cikin dazukan yankin Darazo da Ganjuwa.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Bauchi, DSP Haruna Mohammed ya ce sun samu rahoton sace tsohon dan majalisar daga ofishinsu na Darazo, don haka rundunar ta dukufa wajen aikin gano wadanda suka sace shi, kuma ya roki jama’a su rika ba su labarin duk abin da ba su amince da take-takensa ba.
Ya ce rundunar ta dakile wani yunkuri na kashe Shugaban Jam’iyyar PDP na karamar Hukumar Shira Malam Sama’ila Sambuwal, inda aka kama mutum biyu da bindiga kirar AK-47 guda uku cike da albarusansu, inda ya ce suna ci gaba da bincike kan lamarin.
Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa mazauna garuruwan Soro zuwa Darazo sun jima suna bayar da sanarwar ganin wasu mutane dauke da makamai da motoci da manyan babura suna atisaye a cikin dajin kusa da Kogin Golmo kuma sun sanar da hukuma amma ba wani mataki da aka dauka.
Wakilinmu ya ziyarci garin Darazo inda aka shaida masa cewa a ranar Juma’a da dare wasu mutane sun shiga Darazo suka tayar da wani dan kabilar Ibo mai sayar da magani suka tafi da shi kantinsa suka debi magunguna da allurai da kayan jinya suka dawo dashi gidansa suka wuce cikin motocinsu sanye da kakin soja.
Majiyarmu ta ce hakiman yankin kananan hukumomin Ganjuwa da Darazo ma sun sanar da hukuma kan halin da ake ciki amma ba har yanzu ana ganin wasu mutane suna ci gaba da atisayensu a yankin.