✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace wani babban dan kasuwa a Kebbi

Rahotannin da ke fitowa daga garin Zauro a Karamar Hukumar Birnin Kebbi sun ce an yi garkuwa da wani babban dan kasuwa Alhaji Murtala Zauro…

Rahotannin da ke fitowa daga garin Zauro a Karamar Hukumar Birnin Kebbi sun ce an yi garkuwa da wani babban dan kasuwa Alhaji Murtala Zauro wanda ke harkokin kasuwanci a kasuwar Birnin Kebbi.

Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa an sace dan kasuwar ne jim kadan bayan dawowarsa gida daga kasuwa, inda ya kammala Sallar Isha’i a wani masallaci a kusa da gidansa da ke garin Zauro, sannan ya shiga gida. Majiyar ta ce bayan ’yan mintoti ne sai aka yi masa sallama a gidan da sunan ya yi baki, inda  ya fito domin ganawa da wadanda ke sallama da shi.

Aminiya ta zanta da wani dan uwan dan kasuwar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce “Bayan mun kammala sallar da misalin karfe 8 na dare ne ya shiga gidansa sai kawai wadansu mutane da ba a san su ba suka yi masa sallama ya fito daga nan suka dauke shi. To daga nan ne sai labari ya watsu a cikin garin Zauro da kuma fadin Jihar Kebbi baki daya.”

Majiyar ta ci gaba da cewa “Har yanzu ba mu san ida Alhaji Murtala Zauro yake ba, amma na san cewa jami’an tsaro na bincike don gano inda masu garkuwa da mutanen suka kai shi. Sannan kawo yanzu ko ka buga wayarsa ta hannu a kashe take kuma babu wanda zai iya tabbatar da cewa ga inda yake.”

Aminiya ta nemi jin ta bakin Hukumar ’Yan sandan Jihar Kebbi, inda Kakakinta DSP Danjuma Possi ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce “Hukumar ’Yan sandan jihar na iya kokarinta don ganin ta ceto dan kasuwar daga hannun masu garkuwar da kuma kama su.”

Ya yi kira ga jama’ar jihar su taimaka wa hukumar da bayanan sirri domin taimakawa ga dakile duk wata kafa ta aikata laifuffuka a Jihar Kebbi.