✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace wani Fada a Kudancin Kaduna

A ranar Litinin din nan ce wadansu ’yan bindiga suka sace wani fada mai suna Rabaran John Bako Shekwolo a gidansa da ke a garin…

A ranar Litinin din nan ce wadansu ’yan bindiga suka sace wani fada mai suna Rabaran John Bako Shekwolo a gidansa da ke a garin Ankuwa, a Karamar Hukumar Kaciya da  ke Jihar  Kaduna.

Aminiya ta samu labarin lamarin ya auku ne da misalin karfi 8 na safe lokacin da yake kokarin shiga gidansa jim kadan bayan dawowarsa daga aiki.

Shugaban Cocin  Katolika  Rabaran Daniel J. Kyom wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin a  wata sanarwa da ya fitar ya bukaci al’umma su taya su da addu’a.

Ya ce malamin Kiristan da aka sace shi ne Shugaban Cocin Saint Theresa Catholic da ke Ankuwa kusa da Kaciya.

“Muna bakin cikin sanar da cewa daya daga cikin manyan malamanmu,  John Bako Shekwolo wadansu da ba mu san ko su wane ne ba sun sace shi. Yanzu haka muna neman addu’a daga wajen ’yan darikarmu da sauran mutane domin Allah Ya kubutar mana da shi. Muna kuma rokon wadanda ke rike da shi su taimaka wajen sako shi ba tare da cutarwa ba,” inji shi.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Yakubu Sabo ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce tuni rundunar ta aike da jami’anta da suka hada da shugaban ’yan sandan yankin (DPO) da wadansu kwararru a sashen yaki da garkuwa da  mutane na rundunar da nufin gano duk inda yake tare da kama wadanda suke rike da shi.

Ya ce Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ahmad Abdurrahman ya sha alwashin magance matsalar garkuwa da mutane a jihar tare da yin kira ga jama’a su rika taimaka wa rundunar da bayanai.