Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
An sake bude filin jirgin Kano cikin tsauraran matakan kariya

An sake bude filin jirgin Kano cikin tsauraran matakan kariya

Sakamakon umarnin Gwamnatin Tarayya na sake bude filayen jiragen sama, a ranar Asabar al’amura sun fara daidaita a filin jiragen sama na Malam Aminu Kano da ke Kano.

Jirgin farko mallakin kamfanin Air Peace ne dai ya sauka da misalin karfe 8:40 na safe kuma ya debo fasinjoji ne ‘yan kadan daga Legas.

“Ina matukar farin ciki gaskiya kasancewa jigilar jiragen ta dawo, akalla yanzu rayuwa ta fara komawa kamar yadda aka saba bayan watanni ana zaman kulle”, inji Hajiya Aisha Aminu, daya daga cikin fasinjojin da suka sauka a jirgin na Air Peace yau da safe.

Zirga-zirgar jiragen sama ta cikin kasa dai ta dawo ne a karon farko bayan dakatar da ita da aka yi na tsawon watanni uku a baya sakamakon annobar coronavirus.

Daga bisani kuma wasu jiragen mallakin kamfanonin Air Peace da Azman suka tashi da misalin karfe 11:40 da kuma 11:47 zuwa biranen Legas da Abuja.

Yadda ake tantance matafiya

Aminiya ta lura cewa fasinjoji, ma’aikatan filin da kuma jami’an tsaro na bin dukkan sharuddan yaki da cutar COVID-19 da kwamitin kar-ta-kwana da shugaban kasa ya kafa don yaki da cutar da kuma Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Kasa (FAAN) suka gindaya.

Kusan kowa na amfani da takunkumi, domin kuwa ba a barin kowa ya shiga in ma babu shi.

Kazalika, an samar da sinadarin wanke hannu da kuma sabulu da ruwa a kowanne lungu da sako na filin jirgin, yayin da jami’an tsaro ke tabbatar da cewa kowa sai ya wanke hannuwansa kafin ya shiga wurin tantance masu fasinjoji.

Haka kuma, akan feshe kayan dukkan fasinjoji masu sauka da tashi don tabbatar da cewa ba su shafi kwayar cuta ba, tare kuma da bayar da tazara a kowanne wuri.

Ana yi wa kayan wani daga cikin fasinjoji feshin magani

‘Mun sha wahala lokacin da aka rufe filin’

Da yake tattaunawa da Aminiya, wani mai shagon sayar da kayan masarufi a flilin jirgin Aminu Sale ya koka cewa ‘yan kasuwa sun sha wahala matuka sakamakon dakatar sufurin da aka yi, ko da yake ya bayyana kwarin gwiwar cewa nan ba da jimawa ba al’amura za su daidaita kamar yadda aka saba.

“Yawanci idan lokaci irin wannan ya zo, mukan samu ciniki sosai sakamakon maniyyata aikin Hajji, to amma kasancewar a bana babu, kuma hatta zirga-zirga ta cikin gida ma sai yau take dawowa, muna sa ran nan ba da jimawa ba za a koma harka kamar yadda aka saba a baya”, inji shi.

Kazalika, ma’aikatan kamfanonin sufurin jiragen sun bayyana dawowar a matsayin babbar nasara.

Sagir Abdullahi, wanda shi ne kakakin kamfanin sufurin jirage na Azman a shiyyar Kano ya ce sun fuskanci kalubale matuka, kasancewar harkar sufurin jiragen sama na daya daga cikin harkokin da annobar COVID-19 ta fi yi wa illa.

‘Ba mu kara ko sisi kan kudin tikiti ba’

Kasancewar an ba da umarnin rage adadin mutanen da ake dauka a kowane jirgi domin tabbatar da bayar da tazara, kamfanonin sufurin jiragen sun ce ko sisi ba su kara ba a kan farashin tikitinsu.

Babban manajan kamfanin jiragen sama na Azman, Sulaiman Lawal

Babban manajan kamfanin Azman, Sulaiman Lawal ya shaida wa Aminiya cewa har yanzu farashin kamfanonin bai canza ba.

Ya ce, “Ko da yake gwamnati ta umarci mu rage yawan mutanen da muke dauka, amma mu har yanzu farashin tikitinmu bai canza ba.

“Dukkan kamfanoni sun tafka asara matuka kasancewar dole sai ka rika kashe kudi wajen kula da jirage ko da kuwa ba ka yi amfani da su ba.

“Mun tafka asarar da ba za ta musaltu ba gaskiya”, inji babban manajan.

Mun gamsu da lafiyar filin jirgin Kano – Minista

A wani labarin kuwa, ministan harkokin sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika ya bayyan gamsuwa da shirin da filin jirgin ya yi domin ci gaba da harkokinsa.

Ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika

Ya bayyana hakan ne a Kano lokacin da ya jagoranci wata tawagar gwamnatin tarayya domin duba aikin sabon bangaren sauka da tashin jirage na filin da kuma duba irin shirinsu na dawo da zirga-zirga.

“Ina matukar farin ciki cewa an sake bude wannan sabon filin jirgin bisa kiyaye sharudda na kwamitin kar-ta-kwana, da kuma tabbatar da cewa filin kalau ya ke a ci gaba da amfani da shi”, inji Hadi Sirika.

Wani bangare na sabon sashen kula da sauka da tashin jirage a filin

A nasa bangaren kuwa, jami’in kasa na kwamitin kar-ta-kwana kan yaki da COVID-19, Dr Sani Aliyu ya ce zuwa yanzu sun gamsu da irin matakan kariyar da hukumomin filin da sauran masu ruwa da tsaki a harkar sufurin jiragen sama su ka dauka.

Sauran wadanda suka rufa wa tawagar ministan baya sun hada da shugaban kwamitin sufurin jiragen sama na Majalisar Dattawa, Sanata Smart Adeyemi, da takwaransa na Majalisar Wakilai, Hon. Nnolim Nnaji da kuma sanatocin da ke wakiltar Tsakiya da Kudancin Kano, Ibrahim Shekarau da Kabiru Gaya.