✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake ceto masu ciki 7 daga hannun masu sayar da jarirai a Legas

Hukumar ‘yan sandan Legas tayi nasarar ceto karin mata masu ciki 7 daga Hannun masu gidan sayar da jarirai da ake kira ‘Baby Factory’ a…

Hukumar ‘yan sandan Legas tayi nasarar ceto karin mata masu ciki 7 daga Hannun masu gidan sayar da jarirai da ake kira ‘Baby Factory’ a turance wato masana’artar yin jarirai.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Legas DSP Bala Elkana, ya shaida wa Aminiya cewa, da misalin karfe daya na jiya Laraba wasu mutane suka ankarar da jami’an rundunar inda suka shaida masu ga wasu mata masu ciki su 7 su na gararanba a yankin Oshodi a shiyar Cele da ke kan hanyar Apapa.

“Dukkan su ‘yan shekaru 13 ne zuwa 27, biyar daga cikin su ‘yan jihar Imo ne yayin da ragowar biyun ‘yan jihar Abiya ne, mun kuma same su da karamin yaro mai shekara biyu, zuwa yanzu mun mika su ga hukumar NAPTIP domin basu kulawa a daidai lokacin da muke ci gaba da bincike.” In ji shi.

Ko a makon jiya ma rundunar ta ceto mata masu ciki 19 daga hannun masu hadahadar jariri wadanda ke tara su a gidajen su, idan sun yi ciki sun haife sai su sayar da ‘ya’yan.