✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake kama mutum 28 kan aikata manyan laifuffuka a Jihar Oyo

Rundunar ’Yan sandan Jihar Oyo ta sake kama mutum 28 da take zargi da aikata manyan laifuffuka a sassan jihar. Goma daga cikin mutanen an…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Oyo ta sake kama mutum 28 da take zargi da aikata manyan laifuffuka a sassan jihar. Goma daga cikin mutanen an kama su ne a maboyarsu a garin Oyo lokacin da suka yi fashin wata tirela dauke da sababbin janaretoci 410 da galan 560 na bakin mai da kudinsu ya kai Naira miliyan 40.

Lokacin da yake nuna mutanen da aka kama da  janaretocin kirar SUMEC ga ’yan jarida a ranar Litinin da ta gabata a ofishinsa a Ibadan, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo, Mista Shina Olukolu ya jinjina wa mutanen da suka bayar da labarin da ya kai ga wannan kame. Ya ce samun labarin ke da wuya sai sashen yaki da fashi da makami (SARS) na rundunar ya fara gudanar da aiki inda ya kama mutum  9 da mace daya mai sayen kayan. Ya ce ana ci gaba da bincike don gano sauran mutanen da suka tsere tare da gurfanar da su ga kotu.

Mista Shina Olukolu, wanda ke tare da Mataimakinsa, Attahiru Isa da manyan jami’ansa ya nuna wani mutum mai shekara 47 mai suna Kazeem Ibrahim da ake zarginsa da sayen baburan sata daga hannun barayi. An samu babura kirar Bajaj guda 10 da uku kirar Honda tare da shi bayan kasa yin bayanin yadda ya mallake su. Daga cikin mutanen da aka nuna wa ’yan jarida akwai wadansu Fulani uku masu suna Ahmadu Mudu da Harande Tambaya da Ali Janyo da ake zargins satar mutane da yin garkuwa da su. Sauran mutum 14 da aka kama ana zarginsu ne da aikata fashi da makami da balla kofofin gidaje da shaguna domin satar kayan mutane da kuma yi wa jama’a damfara.

Duk mutanen da aka kama an same su da motocin sata da babura da talabijin da dimbin kudade da manya da kananan bindigogi da harsasai a matsayin shaida. Kwamishinan ’Yan sandan ya ce da zarar sun kammala bincike za a gurfanar da su a  gaban kotu domin yanke musu hukunci.

A lokacin da manema labarai suke yi wa wadanda ake zargin tambayoyi daya bayan daya sun amince tare da furtawa da bakinsu irin hanyoyin da suke amfani da su wajen aikata miyagun ayyukansu.