✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake kama ‘yan China masu hakar ma’adanai a Najeriya

An kama wasu ‘yan China da ake zargi da  hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a Jihar Osun. Rundunar tsaron hadin gwiwa ta JTF da…

An kama wasu ‘yan China da ake zargi da  hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a Jihar Osun.

Rundunar tsaron hadin gwiwa ta JTF da gwamnan jihar Adegboyega Oyetola ya kaddamar a kwanan baya ce ta kama mutane 27 a yankin Ilesa da Ife.

Daga cikin su akwai mutane 17 ‘yan kasar China da wani Dagaci (Baale).

Da yake karin haske a kan lamarin, Mataimakin Shugaban Ma’aikata a ofishin gwamnan, Abdullahi Binuyo, ya ce duk gwamnatin da ta san abin da take yi ba za ta sanya ido tana kallon yadda wasu mutane suke lalata muhallinta ta haramtacciyar hanya ba tare da daukar matakin hanawa ba.

Ya ce bayan zagon kasa da suke yi wa tattalin arziki masu hakar ma’adinan sun gurbata ruwan kogin Osun da dagwalo mai dauke da guba da ya hana amfani da ruwan kogin ta fannin noman rani.

Saboda haka ya ce bayan gurfanar da wadannan mutane a gaban kotu za a tabbatar cewa sun biya diyyar barnar da suka aikata.

Daya daga cikin ‘yan kasar ta China da aka kama mai suna May Zam ta ce ba ta da masaniyar cewa hakar ma’adinan da suke yi ta haramta domin a cewar ta kafin wannan lokaci ta yi a karkashin kamfanonin hakar ma’adinai kuma ba ta taba fadawa cikin irin wannan hali ba.

Ko a baya bayan nan an kama wasu ‘yan kasar China a jihar Zamfara wadanda ake zargi da hakar ma’adanai ta haramtaciyar hanya.