✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake kubutar da dalibai 4 da aka yi garkuwa da su a Kaduna

Rundunar sojojin Najeriya ta sake kubutar ragowar dalibai hudu na makarantar sakandaren Gwagwada a Karamar Hukumar Chikun da ke jihar Kaduna. An yi garkuwa da…

Rundunar sojojin Najeriya ta sake kubutar ragowar dalibai hudu na makarantar sakandaren Gwagwada a Karamar Hukumar Chikun da ke jihar Kaduna. An yi garkuwa da daliban ne a ranar 10 ga watan Oktoba 2019.

Mataimakin Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojojin Kaduna Kanal Ezindu Idimah,  ne ya sanarwa da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a daren ranar Litinin hakan. Inda ya ce a yanzu haka an mika daliban ga iyayen su a Kauyen Gurmi.

‘Yan bindigar dai sun yi garkuwa da dalibai 10 ne a hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar 10 ga Oktoba lokacin daliban ke hanyar su ta zuwa makaranta. Da farko dai rundunar sojojin ta fara kubutar da mutum shida bayan sun tsere da hudu wanda a yanzu haka aka ceto su.