Da Dumi Dumi

An sake nada Sheikh Sudais Shugaban Masallatai Biyu Masu Alfarma

An sake nada Sheikh Abdurrahman Sudais a matsayin Shugaban Masallatan nan  Biyu Masu Alfarma da ke kasar Saudiyya domin kula da wuraren biyu mafi daraja a Musulunci.

Wata sanarwa daga shafin Facebook na Masallatan Haramain- mai suna Haramain Sharifain Facebook page, ta ce sake nadin nasa na kunshe ne cikin wata doka da Masarautar Kasar ta bayar, wacce ‘Sarki Salman Mai Kula da Masallatan ya fitar.’

Sanarwar ta ci gaba cewa, Sheikh Sudais zai sake jagorantar al’amuran masallatan biyu na wasu shekara hudu masu zuwa.

Sheikh-Sudais dai yana shugabancin kula da masallatan ne tun ranar 8 ga Mayun shekarar 2012, kuma shi ne Babban Limamin Masallacin Harami na Makkah.

Sheikh Sudais dai sanannen makarancin Alkur’ani Mai girma ne, kuma mamba a Cibiyar Larabci da ke Makkah. A shekarar 2005 an bayyana shi a matsayin “Musulmi na tara mafiya karfin fada-a-ji a duniya’ da Kwamitin Duniya kan Lambobin Yabo na Alkur’ani da ke Dubai ke shiryawa.

ADVERTISEMENT

Shehin malamin ya samu digiri a bangaren shari’a a Jami’ar Riyadh a 1983, sa’annan ya yi digiri na biyu kan Akida da Shika-shikan Musulunci a Jami’ar Musulunci ta Imam Mohammed bin Saud a  1987. Daga nan sai ya ci gaba da karatun digiri na uku kan Shari’ar Musulunci a a Jami’ar Ummul Kura a 1995, a lokacin yana koyarwa a jami’ar a matsayin Mataimakin Farfesa.

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya