✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake yin garkuwa da Dan Sanda da wasu a Abuja

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da mutum biyu cikin akwai wani jami’in dan sanda mai mukamin…

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da mutum biyu cikin akwai wani jami’in dan sanda mai mukamin Sufeta a unuguwar Rubochi da ke Karamar Hukumar Kuje cikin babban birnin tarayya Abuja.

Wadanda aka yi garkuwan da su sun hada da: Sufeta Selven da Nengba Mundi wadanda aka yi garkuwa da su da tsakar daren ranar Lahadi.

Wani mazaunin unguwar Rubochi, ya bayyanawa Aminiya cewa, ‘yan bindigar sun shiga cikin kauyen garin da misalin karfe 2 na tsakar dare. ‘Yan bindigar sun fara dauke dan sandan daga bisani su shigta gidan Nengba su yi gaba da shi.