Da Dumi Dumi

An sake yin garkuwa da mahaifiyar Siasia

Mutanen da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sake yin garkuwa da mahaifiyar tsohon Kocin Super Eagles Samson Siasia a gidanta a Jihar Bayelsa.

Rahotanni sun ce maharan sun kai farmaki ne a Karamar Hukumar Sagbama da ke Jihar Bayelsa inda mahaifiyar tsohon dan kwallon Super Eagles din ke zaune kuma suka yi awon gaba da ita.

Rahoto ya ce kafin su tafi da ita sun yi ta harbin kan-mai-uwa-da-wabi da misalin karfe 2 na dare a ranar Litinin da ta gabata daga nan suka yi awon gaba da ita.

Har zuwa hada wannan rahoto ba a samu labarin an kama wadanda suka aikata hakan ba ko kuma wurin da suka kai ta.

A watan Nuwamban 2015 ne aka fara yin garkuwa da ita inda sai da iyalanta suka biya Naira dubu 600 a matsayin kudin fansa bayan ta kwashe  kwana 13 a hannun masu garkuwa da mutanen.

ADVERTISEMENT

Zuwa hada wannan rahoto babu labarin ko an kama wadanda suka yi garkuwa da ita ko an sako ta.

Samson Siasia dai ya taba horar da Kungiyar Kwallon Kafa ta Najeriya a matakai daban-daban.  Na baya-bayan nan shi ne horar da kungiyar Dream Team BI inda ya lashe lambar Tagulla a gasar Olamfik da aka yi a Brazil a 2016.

Sannan ya taba horar da kungiyar Super Eagles a lokuta daban-daban.

Share