✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake zuba Naira biliyan 2 a Kamfanin Madara na Sakkwato

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ce Kamfanin Madara na Jihar Sakkwato da ake ginawa a Karamar Hukumar Rabah ya kusa kammala bayan…

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ce Kamfanin Madara na Jihar Sakkwato da ake ginawa a Karamar Hukumar Rabah ya kusa kammala bayan ya kara lashe Naira biliyan biyu.

“Shanun Ajentina da Brazil da za su rika bayar da madarar sun kusa isowa Sakkwato kuma aikin ya kammala saura kadan mu kaddamar da shi domin amfanin jiha da kasa baki daya,” inji Gwamnan.

Gwamnan ya yi wadannan kalamai ne a wurin yekuwar neman sake zabensa a Karamar Hukumar Rabah a Talatar da ta gabata. Ya yi alkawarin sake gina musu babban titin a karamar hukumar da ya hada su da kananan hukumomin Wurno da Bakura.

“Shirye-shirye sun kammala na fara aikin hanya tun daga Lambar Rabah har Bakura, duk lokacin da muka yi zaman Majalisar Zartarwa nan ba da jimawa ba a nan ne za mu ba da aikin hanyar. Za mu ci gaba da aikin da muka soma musamman a bangaren ilimi da lafiya da aikin gona,” inji Tambuwal.

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa a jawabinsa, ya bayyana cewa dukansu tsofaffin da suka rike mukamai sun goyi bayan PDP ne don ci gaban jiha da kasa baki daya. Ya ce akwai bukatar kowa ya bayar da goyon baya ga tafiyar tasu.