Search
Subscribe
An saki Amurkawan da aka yi garkuwa da su

An saki Amurkawan da aka yi garkuwa da su

A Talatar da ta gabata ce Ofishin Jakadancin Amurka ya tabbatar da cewa an sako wasu Amurkawa biyu da aka sace makonni uku da suka gabata a Kudancin Najeriya.

Amurkawan biyu, wadanda suka hada da matukin jirgin ruwan dakon mai, wanda ke dauke da tutar Amurka da kuma babban injiniya, an sace su ne a ranar 23 ga watan jiya a Gabar Tekun Guinea, inda ta’annatin barayin jiragen ruwa ya ta’azzara.
A makon jiya ne ’yan jaridar kafar watsa labarai ta NBC suka gano jirgin ruwan dakon man, mai tsawon kafa 222, malakar kamfanin Lousiana, a tashar jiragen ruwa ta Onne, a yashe shi bisa ruwa.
Jami’a mai magana da yawun ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya, Jen Psaki ba ta bayar da cikakken bayanin yadda aka sako Amurkawan ba. Haka kuma ta ki bayyana sunayen Amurkawan biyu, inda a cewar ta, an yi haka ne saboda bukatar sirri.
“Muna maraba da sakin Amurkawan biyu, wadanda aka sace daga jirgin ruwan dakon mai.” Inji ta.
A cewar kamfanin tsaro na NYA, Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke sahun gaba, inda al’amuran masu sace mutane don amsar fansa suka yi kamari. Ya ta’allaka faruwar haka saboda dukiyar da ake samu daga arzikin mai ba ta isa ga talakawa.
“Talakawan da ke zaune a yankunan da ake hakar mai suna cikin takaici, inda suke ganin ana hako dukiyar mai a kullum amma suna cikin talauci.” Kamar yadda Leke Oyewole, mai ba Shugaba Jonathan shawara ta fuskar al’amuran ruwa ya shaida wa kafar watsa labarai ta NBC.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin