Da Dumi Dumi

An saki Ibrahim Ibrahim da ake zargi da shiga Saudiyya da kwayoyi

Wata kotu a Saudiyya ta wanke malamin nan dan Jihar Zamfara da ake zargin ya shiga kasar da miyagun kwayoyi, wato Malam Ibrahim Ibrahim.

Hukuncin kotun da ke birnin Makkah na zuwa ne bayan da ya shafe shekara uku yana tsare a kasar.

Aminiya ta fahimci cewa sakin nasa, ya biyo bayan azamar gwamnatin jihar da hadin gwiwar Hukumar ’Yan Najeriya Mazauna Ketare (NIDCOM), wadanda  wakilansu suka sauka a Kasa Mai tsarki dauke da hujjojin da aka adana na musamman da ita hukumar NIDCOM ta tanada a shari’ar da aka gudanar ranar Talata.

Kwamishinan Ayyuka na Musamman na Jihar  Zamfara, Alhaji Mohammed Saddik Maiturare ya bayyana labarin sakin Malam Ibrahim din, tun daga can Kasa Mai tsarki a safiyar ranar Talatar.

Da wannan labarin mai faranta rai, Mai taimaka wa Gwamnan Jihar kan Kafafen Watsa Labarai, Zailani Bappah, ya ce kowane lokaci daga yanzu bayan sakin Malam Ibrahim zai iya komawa gida Najeriya domin ya hadu da iyalansa.

ADVERTISEMENT

A baya dai Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa an kama shi ne bisa kuskure.

Ko a bara ma, jami’an tsaron Saudiyya sun kama wata budurwa ’yar Najeriya mai suna Zainab Aliyu jim kadan bayan sun isa Saudiyya don yin aikin Umara bisa zarginta da shiga da miyagun kwayoyi kasar.

Sai dai daga baya hukumomin Saudiyyar sun sake ta bayan da suka tabbatar ba ta da laifi, wadansu suka yi amfani da sunanta a wata jaka.

 

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya