Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An sako dan kasuwar Taraba da aka yi garkuwa da shi

Masu garkuda mutane sun sako dan kasuwar nan na Taraba Usman Mayo wanda aka sace kimanin mako uku da suka gabata a Taraba.

Idan ba a manta ba, Aminiya ta ruwaito wani dan kasuwa da aka sace a Taraba, sannan masu garkuwa da mutanen suka ki sako shi bayan iyalansa sun biya kudin fansa Naira miliyan 100, inda suka bukaci sai an kara musu kudi. Wannan ya sa mutumin ya ce kada iyalansa su kara ko kwabo.

ADVERTISEMENT

Wakilin Aminiya ya jiyo cewa said a aka sake biyan Naira miliyan 5 kafin aka sako dan kasuwar a ranar Talata.

Usman Mayo ya dawo gida, amma yana fama da rashin lafiya wanda hakan ya sa aka wuce da shi asibiti.

ADVERTISEMENT

A lokacin da wakilinmu ya tuntubi Kakakin ’yan sanda na Jihar Taraba, DSP Dabid Misal, ya ce ba su samu labarin ba.