✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sako mahaifiyar Siasia bayan ta shafe kwana 70 a hannun masu garkuwa

Rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa ta tabbatar da sakin mahaifiyar Tsohon Kocin Kungiyar Kwallon Kafa ta Kasa Samson Siasia, mai suna Misis Ogere Beuty Siasia,…

Rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa ta tabbatar da sakin mahaifiyar Tsohon Kocin Kungiyar Kwallon Kafa ta Kasa Samson Siasia, mai suna Misis Ogere Beuty Siasia, mai shekara 79.

An sace Misis Ogere, tun ranar 15 ga watan Yuli bana a gidanta da ke Odini, a Karamar Hukumar Sagbama a Jihar Bayelsa.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar , SP Asinim Butswat ya fitar na cewa, a yanzu haka Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya ziyarci Misis Ogere, bayan an kubutar da ita a yau Lahadi.

https://aminiya.dailytrust.com.ng/siasia-ya-nemi-taimako-bayan-mahaifiyarsa-ta-shafe-kwana-70-a-hannun-masu-garkuwa/