✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sako makusantan Shugaban Karamar Hukumar Bwari da aka sace

Masu garkuwa da mutane sun sako wadansu mata biyu da suka sace a Karamar Hukumar Bwari, Abuja a ranar sabuwar shekara. Matan biyu, daya jami’a…

Masu garkuwa da mutane sun sako wadansu mata biyu da suka sace a Karamar Hukumar Bwari, Abuja a ranar sabuwar shekara.

Matan biyu, daya jami’a ce mai taimaka wa Shugaban Karamar Hukumar, Dokta John Gabaya kan siyasa dayar kuma ’ya ce ga dan uwansa. An sako su ne a ranar Asabar bayan biyan kudin fansa, kamar yadda Aminiya ta samu labari.

An sace matan biyu ne lokacin da suka je kauyen Tokolo a kusa da garin Bwari inda shugaban yake karbar gaisuwar murnar sabuwar shekara.

Aminiya ta samu labarin cewa wani dan uwan shugaban mai suna Ibro Shakogaza da ake zargin shi ne masu garkuwar ke nema, ya samu nasarar tserewa.

Bayanai sun ce matashin wanda ya ji suna tambayar ina yake bayan tsayar da su, ya kutsa ta cikin rafin da ke kusa da inda barayin suka yi dakonsu.

Wakilinmu ya ziyarci Babban Asibitin Bwari a ranar Lahadin da ta gabata inda aka kai matan biyu sakamakon rauni da dayarsu ta ji saboda duka daga ’yan bindigar, yayin da dayar kuma aka ce tana fama da firgita.

Babban Jami’in ’Yan sandan Bwari, CSP Biodun Makanjuola wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce sun fara gudanar da bincike a kai.