Aminiya

An sako ’Yan kasuwan Abuja da a ka sace a Dutsen Zuma

Ragowar mutum biyar daga cikin 19 da a ka sace a kusa da Dutsin Zuma da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, sun koma wajen iyalansu bayan shafe kwana 3 a hannun wadanda suka yi garkuwa da su.

An dai sace mutanen ne wadanda wasu daga cikinsu ‘yan kasuwa ne wasu kuma ma’aikata, a ranar Talata ta makon jiya a kusa da tsaunin wanda ke kusa da sansanin sojoji, da misalin karfe 8 na dare.

ADVERTISEMENT

Daya daga cikin wadanda a ka sacen mai suna Muhammad Mustafa wanda dan kasuwa ne a kasuwar Wuse Abuja, ya shaidawa wakilinmu a yau Laraba cewa, wadanda suka sace su adadinsu ya kai 10 kuma wasu daga cikinsu na sanye da kakin soja da kuma rike da bindigogi, sun wuce dasu zuwa wani jeji da ke da tazarar kamar kilomita 5 daga titin, inda bayan kamar sa’a guda sai su ka sako mutum 14 bayan tantancesu, in ji shi.

Malam Muhammad Mustafa daya daga cikin ‘yan kasuwar Wuse Abuja da aka yi garkuwa da su
ADVERTISEMENT