✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sallami masu Coronavirus uku a Kano

A karon farko an sallami marasa lafiya uku da suka kamu da cutar coronavirus, inda suka bar cibiyar killace masu cutar ta jihar Kano bayan…

A karon farko an sallami marasa lafiya uku da suka kamu da cutar coronavirus, inda suka bar cibiyar killace masu cutar ta jihar Kano bayan da aka tabbatar ba su dauke da kwayar cutar.

Babban jami’in tsare-tsare na kwamitin kar ta kwana kan yaki da annobar coronavirus a jihar, Dokta Tijjani Hussaini ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai.

Dokta Tijjani, ya bayyana cewa an sallami mutanen ne bayan da suka shafe kimanin makonni uku a cibiyar inda kuma sakamakon gwajiinsu har sau biyu ya nuna cewa, ba su dauke da cutar.

Dokta Tijjani, ya jaddada da cewa kwamitinsu yana aiki bisa bin dokokin Hukumar Yaki da Cututtuka Masu yaduwa ta kasa (NCDC) wajen killacewa da kuma sallamar marasa lafiya.

A cewarsa za a sallami wasu marasa lafiyan masu yawa daga cibiyar killacewar a cikin makon nan.

Dokta Tijjani, ya kara da cewa zuwa yanzu jihar tana da yawan masu cutar 365 ciki har da wadanda suka rasu mutum takwas da wadanda suka warke uku.

“Muna nan muna bibiyar mutane 400, da wasu kuma 64 ba su dauke da alamun cutar. bakwai kuma an same su da cutar. Sai dai har yanzu akwai kalubalen rashin samun hadin kai daga alumna akan yadda suke kin yarda a gwada su ko kuma su ki bayyana matsayin lafiyarsu.”

A cewarsa kwanan nan gwamnatin jihar za ta bubbude cibiyoyin karbar samfurin jini a dukkanin kananan hukumomin jihar 44 wanda zai kawo sauki a yakin da ake yi da annobar ta coronavirus.

Jami’in ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da bin shawarwarin masana lafiya ta hanyar bayar da tazara da gujewa shiga cunkoso don a fatattaki yaduwar cutar a tsakanin al’ummar jihar.