An samu ci gaba a harkar sufuri ta kasa – Musa Maitakobi

Alhaji Musa Maitakobi Shugaban Riko na Kungiyar RETEAN ta Kasa
Alhaji Musa Maitakobi Shugaban Riko na Kungiyar RETEAN ta Kasa

Shugaban Kungiyar Masu Motocin Sufuri ta Najeriya (RETEAN), reshen Jihar Legas, kuma Shugaban Riko na Kungiyar ta Kasa, Alhaji Muhammadu Musa Maitakobi ya ce, cikin shekara biyar na mulkin Shugaba Buhari an samu ci gaba sosai a dukkan bangarorin sufuri da suka hada da ta kasa da ruwa da sararin samaniya.

Alhaji Musa Maitakobi ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Legas inda ya ce, tun lokacin da shugaba Buhari ya fara jan ragamar mulkin kasar nan an samu ci gaba a bangaren shimfida manyan hanyoyi da suka karade kasar nan. “Daga nan Kudu maso Yamma har zuwa Arewacin kasar nan za ka ga ana aikin hanyoyi gadan-gadan. Misali in ka duba babbar hanyar Legas zuwa Ibadan hanya ce da take da muhimmanci ta fuskar sufurin kayayyakin masarufi da jama’a ba a nan Kudu maso Yamma kawai ba, har da duk sassan kasar nan, domin duk abin da za a dauko daga tashar ruwa ta nan Legas a yi Arewa da shi ko a Kudu maso Kudu ko Kudu maso Gabas da sauran jihohin da ke Kudu maso Yamma in ka cire Jihar Legas dole ne sai an bi da kayan ta hanyar Legas daga Ibadan. Yanzu in ka lura aikin hanyar ya yi nisa, sannan a Arewa za ka ga aikin tsohuwar hanyar nan wato hanyar kasa ya yi nisa yanzu mafi yawan manyan motocin da ke sufuri kayayyaki zuwa Arewa ta nan suke bi, wannan ci gaba haka yake a sauran sassan kasar nan. Haka abin yake a bangaren sufurin ruwa da na jiragen sama domin saboda ka’idar aikin za ka da ci gaban da aka samu a bangaren sufurin jirage harkar na gudana cikin salama da tsari haka in ka duba bangaren sufurin jiragen kasa aikin layin dogo na zamani da ake shimfidawa daga Kudu zuwa Arewa abin a yaba ne,” inji shi. Ya ce muddin aka kammala aikin harkar sufurin jiragen kasa za ta kankama wanda hakan zai bunkasa tattalin arzikin kasa da rage wahalhalun da ake fama a wannan fuskar domin kayan da tirela 200 za su dauka a lokaci guda jirgin kasa daya zai kwashe su.

Ya ce a wannan tsari za a samu saukin yawan manyan motocin dakon mai da ke faduwa suna haddasa gobara, kuma hakan ba yana nufin kwace wa masu sufurin motoci aikinsu ba ne, domin su ne za su yi dakon kayan daga daffo-daffo zuwa  sassan kasar nan.

Alhaji Musa Maitakobi, ya ce muddin ayyukan da aka dauko na bunkasa harkokin sufuri suka dore za a samu bunkasar tattalin arzikin kasa da wadata.

A makon jiya ne Majalisar Zantarwar Kungiyar RETEAN ta Kasa ta tabbatar wa Alhaji Muhammadu Musa Maitakobi shugabancin rikon kungiyar ta kasa bayan da wakilan majalisar daga jihohi 28 suka rattaba hannu a takardar korar tsohon Shugaban Kungiyar ta Kasa da Sakatarensa.

ADVERTISEMENT

A jawabin da ya yi na karbar ragamar kungiyar Alhaji Musa Maitakobi, ya yi kira ga shugabanninta na jihohi da sauran bangarori a fadin kasar nan su kasance masu yin adalci ga na kasa da su. Ya ce babban abin da zai sanya a gaba shi ne kyautata rayuwar mambobin kungiyar tare da bunkasarta da bunkasa harkokin sufuri tare da wanzar da zaman lafiya da walwala a tsakanin ’ya’yan kungiyar da ilahirin wuraren da suke aiki.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya