✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An samu ci gaba a shekara daya na Gwamna dankwambo – Hajiya Gafa

Wata ’yar siyasa a Jihar Gombe kuma tsohuwar shugabar Mata ta tsohuwar Jam’iyyar ANPP Hajiya Baby Gafa, ta ce a wannan lokaci da Gwamna Ibrahim…

Wata ’yar siyasa a Jihar Gombe kuma tsohuwar shugabar Mata ta tsohuwar Jam’iyyar ANPP Hajiya Baby Gafa, ta ce a wannan lokaci da Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo ya cika shekara daya da sake komawa karagar mulkin jihar an samu nasara da ci gaba sosai irin wanda jama’ar da suka zabi shugaba suke son gani.
Hajiya Baby Gafa, ta ce yanzu haka wasu unguwanni a fadar jihar da ba su taba tsammanin samun titi ba, Gwamna dankwambo ya yi musu, inda ta kawo misali da Unguwar Jekadafari wadanda suka yi adawa amma yanzu unguwar ta zama wata karamar Abuja inda mutanen unguwar suke yabawa kuma da aka zo biyansu diyya an biya su da kyau.
Ta ce Gwamna dankwambo ya yi rawar gani domin da zuwansa ya fara yin dubu a kan hanyoyin raya kasa wanda al’ ummarsa za su amfana a rage zaman banza, inda ta ce yanzu haka ya kafa kwamiti don farfado da kamfanin tumaturi na Manto da ke garin Kumo inda za a dauki ma’aikata fiye da 600. “Mu Gombawa ba mu da bakin magana a kan Gwamna Ibrahim dankwambo domin a halin da ake ciki na rashin kudin yana kokari wajen biyan ma’aikata albashi kuma ya ce kwanan nan za a fara biyan garatuti da fansho ga wadanda suka yi ritaya,” inji ta.
A cewar Baby Gafa, Gwamnan ya bai wa ’yan kasuwa rancen kudi marar ruwa domin su habaka kasuwancinsu. Daga nan ta ce mafarkin al’ummar Jihar Gombe ya tabbata na neman Kwalejin Ilimi ta Jiha inda yanzu haka Gwamnan ya samar da ita kuma ta fara aiki.