Da Dumi Dumi

An samu jinkirin dawo da ‘Yan Najeriya gida daga Afirka ta Kudu

An samu jinkirin dawo da ‘yan Najeriya gida daga kasar Afirka ta Kudu a jirgin kamfanin Air Peace Airlines sakamakon jinkiri wajen binciken tantance wadanda za a dawo da su.

A cewar jami’an ma’aikatar kasashen waje da ke birnin Johannesburg da ke Afirka ta Kudu, na cewa an tsara tashin jirgin Air Peace da ‘yan Najeriyar da misalin karfe 9 na safiyar yau, amma har yanzu jirgin bai tashi da kowa ba yana kasa.

Jami’an sun ce, an tantance fasinjoji 84 cikin 313 cikin rukunin farko da za a dawo da su gida Najeriya a yanzu haka.

Sai dai jami’an tsaron shige da fice na kasar sun ce an samu jinkirin ne, sabod matsalar na’urar tantancewar.

ADVERTISEMENT
Share